Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ya rubuta a shafinsa na Telegram cewa, "Rasha tana da amintattun abokantaka, ba kawai a sararin samaniyar Tarayyar Soviet ba, har ma a China, kudu maso gabashin Asiya da Afirka, kuma wadannan manyan kasuwanni ne."
Ya kara da cewa, "Mun fuskanci rikice-rikice, takunkumi, barazana da matsin lamba na siyasa fiye da sau daya, a 2008, 2014 da 2018, da kuma takunkumi daban-daban da aka kakaba mana a baya.
Amma mun daina jin tsoro da dadewa, sannan ba da jimawa ba abokan adawar mu da kansu suka zo mana da bukatu, a koma kan teburin tattaunawa kan dukkan batutuwa.
"Takunkumi na baya sun tilasta mana haɓaka hanyoyin shigo da kayayyaki a duk masana'antu, Majalisar zartaswa ta riga ta ɗauki matakai masu amfani don tallafa wa jama'a da tattalin arzikin, Wannan yana faruwa a yanzu," in ji shi.
Medvedev ya bayyana cewa, a hankali ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fara ja da baya daga matsayinta, lokacin da jami'ai a Washington suka yi kalamai na tsanaki game da yiwuwar dage yawancin takunkumin da aka kakabawa Rasha.342/