Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Parstoday
Asabar

19 Maris 2022

19:33:43
1240898

​Shugaban Kasar China Ya Bukaci A kawo Karshen Yakin Ukrain Da Gaggawa

Shugaban kasar China Xi Jinping ya bukaci a kawo karshen yakin da ake fafatawa tsakanin Rasha da Ukrain, ya kuma bukaci bangarorin biyu su rungumi tattaunawa don warware matsalolin da ke tsakaninsu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da tokwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta kafar hotunan Bidiya.

Xi ya bukaci kasashen Amurka da China su yi aiki kafad da kafada don don tabbatar da zaman lafiya a duniya, wanda nauyi ne wanda kasashen duniya suka dora a kansu.

Kafin ganawar wacce ta dauki kimani sa’o’ibiyu, gwamnatin Amurka ta gargadi kasar Rasha dangane da taimakawa Rasa wajen kaucewa radadin takunkuman da kasashen yamma suka dora mata.

342/