Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

17 Maris 2022

18:40:57
1240264

Mali Ta Rufe Gidan Radiyon Faransa Rfi, Da Tashar France24

Gwamnatin Mali ta bada umarnin rufe gidan radiyon faransa rfi da kuma tashar talabijin ta france24.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wata sanarwa da ta fitar gwamnatin Malin, ta ce an dakatar da wadanan kafofin yada labaran har sain abunda hali ya yi.

Sannan an harmtawa duk wata kafa ta kasar Malin, watsa shirye shiyen wadanan tashoshin a cikin gida.

Malin ta daganta matakin da furucin da kwamishiniyar hukumar kare hakkin bil adama ta MDD, ta yi, da rahoton HRW da kuma wani rahoto da gidan radiyon rfi, ya watsa wanda a ciki ta ce ana zargin sojojin kasar na FAMa da aikata laifuka ciki har da kisan kai, wanda Malin ta ce ana hakan don batawa sojojinta suna, da neman wargaza mulkin rikon kwarya na kasar da neman haddasa fitina, ta hanyar cusa kiyaya da kuma kara wa zawo ruwa game da matsalolin tsaro da kasar ke fama dasu.

342/