Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

17 Maris 2022

18:40:24
1240263

Kwamitin Tsaro Zai Yi Zama, Game Da Batun Ukraine

A wani lokaci yau Alhamis ne kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, zai yi wani zama game da batun tabarbarewar al’amuran jin kai a Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kasashen yamma bakwai ne da suka hada da Biritaniya, Amurka, Albaniya da faransa da Norwey da kuma Irdande ne suka bukaci zaman na kwamitin tsaron na MDD, a yayin da aka shiga kwana na 22 na rikicin Rasha da Ukraine.

Hukumomin Ukraine dai sun zargi sojojin Rasha da kai hari kan wani dakin kallon wasan barkwanci dake birnin Marioupol, inda mutane fiye da dubu guda suke gudun hijira, lamarin da da’irar birnin ta ce ba za ta tab yafewa ba, duk da cewa har yanzu ba’a fitar adadin mutanen da lamarin ya rusa dasu ba.

A wani labarin kuma kotun kasa da kasa ta ICJ, wacce take zaman babbar kotun MDD ta bukaci kasar Rasha da ta dakatar da kutsen da ta ke a Ukraine.

342/