Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

17 Maris 2022

18:37:45
1240260

Fadar Mulkin Kasar Rasha Ta “ Kremlin” Ta Ce: Amurka Kasa Ce Da Ta Kashe Dubun Dubatar Mutane A Duniya

Kalaman na fadar mulkin Rasha, ta Kremlin ya zo ne a matsayin mayar da martani ga shugaban kasar Amruka joe Biden wanda ya siffata shugaba Vladimir Putin da cewa mutum ne wanda ya aikata laifukan yaki, inda ta ce; Ko kadan ba zance ne da za a lamunta da shi ba, daga bakin shugaban kasar da ta kashe dubun dubatar mutane a fadin duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A jiya Laraba ne dai shugaban kasar ta Amurka wanda ya amsa tambayoyi daga manema labaru ya bayyana shugaban kasar Rasha a matsayin wanda ya aikata laifukan yaki.

Kakakin fadar mulkin Rasha Dmitry Peskov ya bayyana cewa; Zance ne wanda ba za a taba yarda da shi ba, ba kuma za a yafe shi ba, ace ya fito ne daga bakin shugaban kasar da bama-bamanta su ka kashe dubun dubatar mutane a fadin duniya.

A jiyan dai Amurka ta sanar da cewa za ta taimakawa kasar Ukireniya da makaman da za ta yaki Rasha da su, lamarin da ake ganin zai iya tsawaita lokacin yakin, ya kuma iya fadada fagensa.

342/