Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Alhamis

17 Maris 2022

17:57:29
1240251

Sakon Ta'aziyyar Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Bait Na Duniya (AS) Ta Rasuwar Ayatullah Alawi Gorgany

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Bait Na Duniya (AS) ya fitar da sakon ta'aziyyar rasuwar Ayatullahi Haj Sayyid Muhammad Ali Alawi Gorgany

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Bait Na Duniya (AS) ya fitar da sakon ta'aziyyar rasuwar Ayatollah Hajj "Sayyed Muhammad Ali Alawi Gorgany".

Nassin sakon Ayatullahi "Reza Ramezani" shi ne kamar haka;

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

An karbo daga Aba Abdullah al-Sadik (a.s) ya ce: “Idan Mumini, masanin fikihu ya mutu, musulunci ya samu baraka ta yadda babu wani abu da zai toshe wannan barakar.

Rasuwar malamin Mujahid kuma ma'abocin addini, Ayatullahi Haj Sayyid Muhammad Ali Alawi Gorgany (RA) - wanda ta aiku jim kadan bayan rasuwar marigayi Ayatullahi Safi Golpayegani - ya sake haifar da wata babbar illa da baraka ga duniyar Shi'a.

Marigayi Saeed wanda ya yi amfani da sahihiyar igantaccen tushen fikihun iyalan Annabi Muhammad (S.A.W) a makarantun hauza na Kum da Najaf, ya shayar da masu kishinsa da dalibansa da wadannan ilimomi masu tsafta ta hanayar koyarwa tsawon shekaru.

Hidimominsa masu kima na inganta Ilimomin kur'ani da Iyalan Annabi Sawa, rubuce-rubucen kur'ani, ruwaya, fikihu, ka'idoji na dabi'u da halayya, hidimomin sadaka iri-iri a garuruwa da kauyuka da ayyuka daban-daban da ya bari, su ne ragowar ayyukan Alkhairinsa da suka wanzu.

Kyawawan halaye na marigayi Ayatullahi Alawi Gorgany - kamar zurfafa tunani da tunani zuwa ga Ma’asumai (AS), adabi, kaskantar da kai, kyawawan halaye abin koyi, farin jini da sauki - za su zama abin koyi ga malamanmu da manyanmu.

Baya ga goyon bayan tsari mai tsarki na Jamhuriyar Musulunci, ya kuma kasance jigo a cikin lamurran da suka shafi duniyar Musulunci da nuna rashin yarda da irin zaluncin da akewa 'yan Shi'a na duniya; Kuma ya kasance mai tausasawa da kula da Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya da ayyukanta iri-iri.

Dangane da wannan rashi mara misaltuwa ga halarar Imam Qudubin duniya waliyul Asr (as) Da Jagoran juyin juya halin Musulunci, da manya-manyan Marajio'in da ake koyi da su, na makarantun Hauzozin Qum da Najaf, mutanen lardin Golestan, gida madaukaki na Alawi Gorgany, ga daukacin dalibai, da masu taqlidi da shi, mabiyansa na gaskiya na ke mika ta'aziyyata.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba wa wannan ma’abocin daukaka daukaka tare fatan haduwa da kakanninsa tsarkaka, ga kuma iyalansa wadanda suke raye ina mai yi masu gaisuwa da basu hakuri.

Ga Allah Mu Ke Kuma Gare Shi Muke Komawa

Reza Ramezani
Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Bait Na Duniya (AS
25/Isfand/ 1400Hs

Yana da kyau a ambaci cewa Ayatollah Sayyid Muhammad Ali Alawi Gorgany daya daga cikin Maraji'ai da ake koyo dasu kuma babban malamin makarantar hauza na birnin Qum

ya yi bankwana da Duniya yamamcin ranar Talata 15 ga watan Maris 2022.

342/