Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

16 Maris 2022

19:31:57
1239954

An Ayyana Dokar Hana Fita Ta Sa’o’I 36 A Birnin Kiev Na Ukraine

An ayyana dokar hana fita ta tsawon sa’o’I 36 a Kiev babban birnin kasra Ukraine, a daidai lokacin da bayanai ke cewa ana kai hare hare a wasu unguwanni na birnin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan dai na zuwa ne a yayin da aka shiga kwana na 21 na rikicin Rasha da Ukraine din.

A wani lokaci yau ake sa ran bangarorin zasu sake komawa bakin tattaunawa a karo na biyar.

Hukumar kula da kaurar jama’a ta MDD, ta bayyana cewa sama da mutum miliyan uku ne suka tsarewa rikicin Ukraine.

Haka zalika Kimanin mutane 20,000 ne suka samu fida daga birnin Marioupol a ranar Talata ta hanyoyin da akayi tanadi domin ayyukan jin kai.

342/