Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shi dai Mokom da sauran ‘yan kungiyarsa ana zarginsu da aikata laifuka akan bil’adama a birnin Bangul na kasar Afirka Ta Tsakiya a shekarun 2013 da kuma 2014,kamar yadda sanarwar kotun ta manyan laifuka mai matsuguni a birnin Hague ta bayyana.
Kasar Afirka Ta Tsakiya Ta Fada Cikin Rikici Da Fadace-fadace bayan kifar da shugaban kasar Francois Bozize a 2013, ta hannun kungiyar Seleka.
Tun bayan da kasar ta sami ‘yanci daga ‘yan mulkin mallakar Faransa a 1960’s, ta kasance mai fama da talauci duk da dimbin arzikin da Allah ya huwace mata.
342/