Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

14 Maris 2022

17:51:58
1239224

An Koma Kan Teburin Tattaunawa Tsakanin Rasha Da Ukrain A Kasar Belerus

A safiyar yau Litinin ce tawagogin tattaunawa kan tsagaita budewa juna wuta a yakin da ake fafatawa tsakanin sojojin Rasha da na Ukrain a cikin kasar Ukrain suka koma kan teburin tattaunawa a yankin Gomel na kasar Belarus.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban tawagar tattaunawar kasar Ukrain Mykhailo Podolyak yana fadar haka a shafinsa na Twitter a safiyar yau Litinin.

Ya kuma kara da cewa wannan shi ne taron tattaunawan kan tsagaiuta budewa juna wuta na 4 kenan tun bayan fara yakin kwanaki kimani 18 da suka gabata.

Banda haka Mykhailo Podolyak ya ce banda haka an sami ci gaba a tattaunawar baya, kuma a cikin ‘yan kwanakin masu zuwa muna saran za’a sami ci gaban da bangarorin biyu zasu amince a kansu.

Har’ila yau a bangaren kasar Rasha kuma, kakakin gwamnatin kasar Dmitry Peskov ya bada sanarwan cewa za’a koma kan teburin tattaunawa a safiyar yau Litinin a kasar Belerus kamar yadda aka saba.

342/