Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

14 Maris 2022

17:46:00
1239217

Tsohon Shugaban Amurka Ya Kamu Da Cutar Korona

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama, ya harbu da cutar korona.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Obama ya bayyana a jiya Lahadi cewa, gwajin da aka yi masa ya tabbatar da harbuwarsa.

Amma ya ce, gwajin da aka yiwa mai dakin sa, Michelle, ya nuna ba ta dauke da cutar.

Obama wanda a yanzu ke da shekaru 60, ya kasance shugaban Amurka na 44, kuma bakar fata na farko da ya mulki kasar tsakanin shekarun 2009 zuwa 2017, ya bayyana cewa da shi da mai dakinsa duk sun karbi alluran riga kafin cutar ta korona.

342/