Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

12 Maris 2022

13:42:17
1238427

Putin Ya Ce Ana Samun Ci Gaba A Tattaunwar Da Ake Da Ukraine

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce an samu dan ci gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, yayin da matakin sojin da Moscow ta ce ta dauka kan Ukraine din ya shiga mako na uku.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ‘’An samu wasu sauye-sauye masu kyau, kamar yadda masu tattaunawa daga bangarenmu suka ba ni rahoto," in ji Putin yayin wata tattaunawa da takwaransa na Belarus, Alexander Lukashenko, yayin wata zantawa ta kafar bidiyo a ranar Juma'a, saidai ba tare da yin karin haske ba.

Ya ce "a halin yanzu ana gudanar da tattaunawar a kusan kowace rana," ya kara da cewa zai sanar da Lukashenko game da tsarin tattaunawar.

Kalaman na Putin na zuwa ne kwana guda bayan ganawar da ministocin harkokin wajen Rasha da Ukraine suka yi a birnin Antalya na Turkiyya ba tare da an samu wani sakamako ba.

342/