Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

9 Maris 2022

16:08:53
1237738

Saudiya Da, UAE Sun Ki Amsa Kiran Wayen Biden Kan Tsadar Farashin Mai A Kasuwannin Duniya

Sarakunan kasashen Saudiya da Hadaddiyar daular larabawa ko UAE sun ki amsa kiran shugaban Amurka Joe Biden ta wayar tarho a dai dai lokacinda shugaban yake kokarin ganin ya rage tsadar man fetur a kasuwannin duniya.

Jaridar The Wall Street Journal (WSJ) ta Amurka ta bada labarin a jiya Talata ta kuma kara da cewa sarakunann biyu suna da matsala da shugaban na Amurka, wanda ya ki basu goyon bayan da suke so a yakin da suke fafatawa a kasar Yemen.

Har’ila yau yarima mai jiran gadon sarautar kasar Saudia yana bukatar kamuni daga gwamnatin kasar Amurka dangane da kissan Jamal Khashagji amma shugaban yaki ya tanka masa.

Har’ila yau kasar Saudiya tana son gwamnatin Amurka ta taimaka mata kan shirinta na makamashin nukliya, a dai dai lokacinda Iran ta yi nisa da na tsa shirin. Kuma mai yuwa a cikin yan kwanaki masu zuwa za’a dauke mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata.

Sai dai duk hada a safiyar yau Laraba shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bada sanarwan cewa gwamnatin Amurka ta dakatar da sayen danyen man fetur daga kasar Amurka.

342/