Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

9 Maris 2022

16:07:53
1237737

'Yan Kenya A Ukrain Sun Ce Gwamnatin Kasarsu Ta Yi Watsi Da Su

‘Yan kasar Kenya wadanda suke karatu a kasar Ukrain sun bayyana cewa gwamnatin kasarsu ta manta da su, don bata yi wani abu na taimaka masu su fita cikin mummunan halin da suke ciki a kasar Ukrain ba.

Jaridar Nation ta kasar Kenya ta bayyana cewa mafi yawan daliban jami’o’ii daga kasar Kenya suna karatu ne a birnin Sumy da ke kusa da kan iyakar kasar Rasha.

Wani daliban da aka mrusta da shi ya ce a farkon yakin an ce masu su zauna a cikin gidajensu, ba wana zai taba su. Amma daga baya aka ce masu dole ne su bar gari don sojojin rasha sun yiwa garin Sumy kawanya mai yuwa su kwace garin da karfi.

A halin yanzu dai gwamnatin kasar Rasha ta bayyana cewa zata tsagaita bude wuta a yankin don bawa fararen hula wadanda aka rutsa da su a yancin su fice. Har’ila yau saojojin Rasha sun bayyana cewa sojojin Ukrain suna amfani da fararen hulan a matsayin garkuwa don hana sojojin Rasha kai masu farmaki.

Labaran sun kara da cewa kimani daliban jami’o’ii daban daban daga kasashen waje 2000 ne yakin Rasha a Ukrain ya rutsa da su a cikin kasar.

342/