Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

9 Maris 2022

16:00:43
1237728

Amurka Ta Haramta Shigo Da Man Fetur Da Gas Din Rasha

Bayanai daga Amurka ne cewa, shugaban kasar zai sanar da wannan rana cewa, kasar za ta haramta shigo da man fetur din Rasha,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cewar Bloomberg, Joe Biden, zai sanya takunkumi kan man fetur da kuma gas na Rasaha, saboda yakin da ta shelanta kan Ukraine ba gaira ba dalili, inji wata sanarwa da fadar White House ta fitar.

Kafin hakan dai wannan batu ya janyo rarrabuwar kai tsakanin kasashen turai, inda wasu ke cewa su kam ba zasu mutunta wannan matakin ba.

Jamus ta bakin ministocin kudi da kuma na harkokin wajen ta, sun yi watsi da shawarar da wasu kawayensu na turai da Amurka suka fara yi tunda farko na a sanyawa Rashar takunkumi a fannin albartun mai.

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock, ta ce wannan tunanin ba shi ne mafita ba, kuma kada a yi tsammanin irin wannan matakin zai dakatar da tankokin yakin Rasha ba.

342/