Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

9 Maris 2022

15:58:32
1237726

Rasha Ta Bude Wasu Hanyoyin Jin Kai Domin Fitar Da Fararen Hula A Ukraine

Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar cewa ta bude wasu hanyoyin jin kai domin fararen hular Ukraine su fice daga garuruwan da ake gwabza fada, a daidai lokacin da kuma dakarunta zasu tsagaita bude wuta.

Matakin daya fara aiki da safiyar yau ya shafi garuruwan da suka hada da Cherhihiv da Sumy da Kharkiv da Mariupol da kuma Kyiv babban birnin kasar.

Saidai an samu rahotanni bude wuta, inda bangarorin ke zargin ko wanne da keta yarjejeniyar da aka cimma.

Wannan dai na zuwa ne bayan da masu shiga tsakani na kasashen Rashar da Ukraine, suka kammala zagaye na uku na zaman sulhu, saidai suka gaza cimma wani gagarumin sakamako na tattaunawar zaman lafiya da suka yi a kasar Belarus jiya Litinin.

Mai taimakawa shugaban kasar Rasha kana jagowan tawagar Rasha a tattaunawar Vladimir Medinsky, ya bayyana cewa, tattaunawar za ta ci gaba a kan batutuwan siyasa da na soja.

Bangarorin biyu sun yi magana kan batun kwashe fararen hula, kuma bangaren Ukraine ya tabbatar wa Rasha cewa, hanyoyin kai kayayyakin jin kai za su fara aiki a yau Talata.

342/