Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

19 Faburairu 2022

13:35:56
1231247

Rasha Ta Bukaci Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Kasar Siriya

Gwamnatin kasar Rasha ta jaddada kira ga gwamnatin kasar Amurka na ta janye sojojinta daga kasar Siriya, don mutunta hurumin kasar kasar da kuma bata dama ta warware matsalolin zamantakewa wadanda kasar take fama da su a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto wakilin kasar Rasha a yankin gabas ta tsakiya da kuma Afirka kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Rasha Mikhail Bogdanov yana fadar haka wa kamfanin dillancin labaran AT.

Labarin ya kara da cewa wasu kungiyoyin sun dogara da samuwar Amurka a kasar Siriya don wanzuwarsu, don matukar Amurka tana nan to ba’a sami zaman lafiya a kasar ba, kuma babu damar sake gina kasar da kuma dawowar yan gudun hijira zuwa gidajensu ba.

342/