Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

15 Faburairu 2022

16:17:00
1229874

Canada : An Ayyana Dokar Gaggawa Domin Murkushe Masu Zanga-zanga

Firaministan Canada, Justin Trudeau, ya ayyana wata dokar gaggawa domin taimakawa lardunan kasar, kawo karshen shingayen da aka kafa da jerin gwanon motoci sanadiyyar zanga-zanga adawa da dokar korona.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Justin Trudeau, ya bayyana yayin wani taron manema labarai cewa, ya ayyana dokar ne karon farko a tarihin kasar, domin ba gwamnatin tarayya karin iko na wucin gadi, da nufin magance batutuwan dake akwai.

Yana mai cewa, matakin zai shafi yankuna masu bukata ne kadai, ba dukkan kasar ba.

Dokar, wadda ta maye gurbin dokar yaki ta 1980, na samar da iko na musamman domin tunkarar yanayin gaggawa dake shafar walwalar jama’a kamar aukuwar iftila’i da barkewar cututtuka da rikice-rikice da matsalolin gaggawa a kasashen waje da kuma barkewar yaki.

342/