Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

11 Faburairu 2022

13:06:45
1228401

​Guterres: Kasashen Duniya Ba Su Alkawalinsu Na Samar Da ‘Yantacciyar Kasar Falastinu Ba

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce halin da ake ciki a yankunan Falasdinawa da aka mamaye na ci gaba da zama babban kalubale ga zaman lafiya da tsaro a duniya, kuma ba a cika alkawarin da kasashen duniya suka yi na samun ‘yancin cin gashin kai ga Falastinawa ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Shafin Arabi Jadid ya bayar da rahoton cewa, a yayin bude taron farko na kwamitin majalisar dinkin duniya a sabuwar shekara domin nazarin halin da al'ummar Palastinu ke ciki da kuma hakkokinsu da bai kamata a tauye musu ba, Antonio Guterres ya ce: “Yanayin siyasa, tattalin arziki da tsaro a daukacin yankunan Falasdinawa da aka mamaye suna da kara muni, kuma Palasdinawa na fama da tashe-tashen hankula da rashin tsaro.”

Antonio Guterres ya bayyana a yayin bude taron farko na kwamitin Majalisar Dinkin Duniya cewa, Shekarar tana tattare da abubuwa na yin nazari kan halin da al'ummar Palastinu ke ciki da kuma hakkokinsu da ba za a taba mantawa da su ba.

Guterres ya jaddada cewa, gamayyar kasa da kasa na bukatar kokarin hadin gwiwa domin warware rikicin, da kuma kawo karshen mamayar yankunan Falastinawa kamar yadda kudurorin MDD, da dokokin kasa da kasa, da kuma yarjejeniyoyin bangarorin biyu suka tanada.

Babban magatakardar ya kuma jaddada cewa, manufar ita ce kiyaye gwamnatocin bangarorin biyu na Isra'ila da kuma gwamnatin Palasdinu mai cin gashin kanta, da kuma kasancewarsu kasashe biyu da za su zauna lafiya da juna da kuma aiki kafada da kafada, da mutunta iyakokin da ke kan iyakarsu da aka shata tun watan Yunin 1967, tare da birnin Kudus a matsayin babban birnin hadin gwiwa, a cewarsa.

Guterres ya jaddada bukatar dakatar da wuce gona da iri, da kuma tallafawa ci gaban tattalin arzikin yankin Gaza, da kuma dakatar da ayyukan tsugunar da Falastinawa da aka raba da muhallansu, wanda hakan ya saba wa ka’ida.

342/