Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

11 Faburairu 2022

13:00:47
1228395

Halin Da Ake Ciki A Yankunan Palasdinawa Babban Kalubale Ne Ga Zaman Lafiya Da Tsaro Na Duniya

Babban magatakardar Majalisar dinkin duniya Antonio Gutteres ya fadi cewa yanayin da yankunan falasdinawa da Isra’ila ta mamaye yana ci gaba da zama babban barazana da kalubale da zaman lafiya da tsaro na duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da yake Magana a gaban kwamitin kan batun da ya shafi hakkokin falasdinawa Gutteres yayi kira da a dauki mataken gaggawa na shawo kan rikicin da kuma kawo karshen mamayar yankin dai dai da kudurin majalisar dinkin duniya da aka cimma matsaya akai.

Har ila yau ya fadi cewa warware rikicin ta hanyar kafa kasashen biyu masu cin gashin kai shi ne mafita .

Sai dai yawan tashe -tashen hankula da ke faruwa da samame da sojojin isra’ila ke kaiwa da yake sandiyar rasa rayuka na zama babban abin damuwa a halin yanzu.

Daga karshe ya nuna cewa wajibi ne Isra’ila ta dakartar da dukkan gine -gine ba bisa ka’ida ba da ta ke yi, kuma ya bukaci a dauki matakin farfado da mataken siyasa da za su taimawa wajen inganta halin tattalin arziki da na jin kai ga Alummar paladinu.

342/