Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

9 Faburairu 2022

13:27:22
1227867

​MDD: Kwamitin Tsaro Ya Kasa Cimma Matsaya Kan Juyin Mulki A Burkina Faso

Kwamitin tsaro na MDD ya gudanar da taro a kebe don tattauna batun juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Burkina Faso, amma kwamitin ya tashi ba tare da an cimma wani abu da za’a yi kan juyin mulkin ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Jaridar ‘Nation’ ta kasar Kenya ta bayyana cewa bayan taron, kasar Ghana wacce take cikin kwamitin ta rabawa kafafen yada labarai wani rahoto ya ya bukaci sojojin su farfado da kundin tsarin mulkin kasar sannan su saki tsohon shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore wanda suke tsare da shit un bayan juyin mulkin.

Banda haka rahoton ya kara da cewa kwamitin yana goyon bayan shirin kungiyar ECOWAS a kan juyin mulkin na Burkina Faso.

342/