Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

8 Faburairu 2022

14:09:36
1227453

Wani Jami’in Amurka Ya Bayyana Ficewar Trumph Daga Yarjejeniyar Nukiliyar Iran A Matsayin Wauta

Da yake bayani da manema labarai kakakin maka’ikar wajen Amurka Ned Price yace matakin da tsaohon shugaban Amurka Donald Trumph ya dauka na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar iran a shekara ta 2018 Wauta ce sosai, sai dai ya rage wa iran ta dauki matakin da zai kai ga farfado da yarjejniyar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -A ranar jumaa da ta gabata ce sakaren harkokin wajen Amurka Antony blinken ya sanar da sake dawo da takunkumin da aka sanya wa Iran dake da alaka da shirinta na nukiliya , dagewar da wa’adinta ya kare tun zaman tsohon shugaban Amurka trumph a wani bangaren na matsin lamba kan kasar iran bayan ficewa daga yaejejeniyar

Anata bangaren kasar iran da take mayar da martani kan batun ta fadi cewa sanar da cire takunkumi ta fatar baki bai wadatarba sai idan an gani a aikace a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa a birnin vianna.

Tuni da gwamnatin Biden take sokan matakin matsin lamba da gwamnati Trumph ta dauka kan kasar Iran sai dai babu wani mataki da ta dakuka na kawo karshensa har yanzu.

342/