Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : IQNA
Laraba

2 Faburairu 2022

19:06:59
1225297

Al-Azhar ta yaba da ayyana ranar yaki da ayyukan kyamar Musulunci a kasar Canada

Al-Azhar ta yaba da matakin da gwamnatin Canada ta dauka na ayyana ranar 29 ga watan Janairu a matsayin ranar yaki da ayyukan kyamar Musulunci ta kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cewar shafin Al-Wafd, masu sanya ido na cibiyar Azhar sun  yaba da matakin da gwamnatin Canada ta dauka, wanda ya zo daidai da ranar cika shekaru biyar da harin ta'addanci da akai kan masallata a babban masallacin birnin Quebec a ranar 29 ga watan Janairun 2017.

Harin da aka kai a lokacin ya yi sanadin mutuwar mutane shida tare da raunata wasu masu ibada da dama.

A tarukan tunawa da zagayowar ranar da aka kai harin, firaministan Canada ya yi Allah wadai da ayyukan kyamar Musulunci a kasar Canada tare da bayyana matakin da gwamnatin kasar ta dauka na ayyana ranar 29 ga watan Janairu a matsayin ranar yaki da kyamar Musulunci ta kasa.

Kungiyar Al-Azhar Watchdog ta masu sanya ido na cibiyar ilimi ta Azahar ta yaba da kokarin da gwamnatin Canada ke yi na dakile kyamar Musulunci da Musulmi, inda ta bayyana wannan kiyayya a matsayin wani nau'i na wariya da ke haifar da tsatsauran ra'ayi da ta'addanci.

Kungiyar ta jaddada bukatar sauran kasashen yammacin duniya da su bi sahun  gwamnatin Canada wajen daukar irin wannan mataki,  domin dakile wannan lamari na kyamar addinin Islama, kungiyar ta ce: Wannan lamari yana da mummunan tasiri ga hadin kan al'ummomi kuma yana iya haifar da rugujewar al'ummomi.

342/