Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ya kara da cewa kasar Iran tana karba daururuwan Afghnawa yan gudu hijira duk da takunkumin tattalin arziki da take ciki, da kuma rashin samun hadin kai hukumomi na kasa da kasa da alhakin hakan ya rataya awuyansu, wanda a lokacin yanayi na sanyi ma takara rubanya ayyukan jinkai da take yi a kasar ta Afghanistan
Da yake bayani a wajen taron kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya a fakon makon nan Guterres ya fadi cewa bazan taba mantawa da irin karamcin da kasashen iran iran suka nuna ba yadda suka kwashe shekaru suna maraba da miliyoyin yan gudun hijirar kasar Afghanistan a kasarsu.
Daga karshe ya nuna cewa akwai bukatar hada hannu tsakanin Majalisar da alummar duniya wajen ganin an fitar da kasar Afghanistan daga mawuyacin halin da take ciki.
342/