Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

22 Janairu 2022

12:52:29
1221344

M D D Ta yi Tir Da Harin Da Da Kasar Saudiya Ta Kai A Yamen

Rahnotanni da muka samu sun nuna cewa Majalisar dinkin duniya ta yi Tir da harin da Dakarun kawance da kasar Saudiya ke jagoranta suka kai a birnin Sa’ada dake Arewacin kasar Yamen inda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama ,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jiragen yakin dakarun kawance dake jagoranta sun kai hari a wani gidan yari inda suka kashe akalla mutane 70 tare da jikkata 140, kuma akwai yi wuwar adadin wadanda suka mutu ya karu musamman yadda raunin da wasu suka ji ya yi muni matuka

A jiya juma’a ce sakatare Janar din Madd Antonio Gutress tab akin mai Magana da yawunsa Stephen Djuricc yace majalisar dinkin duniya ta yi tir da harin da aka kai a kan gidan yari a Saada da wasu yankunan day a hadda mutuwar mutane da dama mafi yawancinsu mata ne da Yara kanana,

Daga karshe ya yi kira da a gudanar da binciken kwakwaf cikin gaggawa kan abin day a faru domin daukar matakin da ya dace akai, kana ya bukaci a gaggauta kawo karshen hare-haren.

342/