Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

18 Janairu 2022

13:57:26
1220232

​Oxfam: Sakamakon Bullar Cutar Corona Manyan Masu Kudi Na Duniya Sun Rubanya Arzikinsu

Wani rahoton kungiyar Oxfam ya sanar da yadda attijaran Duniya 10 suka rubanya arzikinsu cikin shekaru 2 da suka gabata na annobar coronavirus da ta jefa miliyoyin jama’a ga kangin talauci da yunwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahoton wanda kungiyar ta fitar yau litinin, ta ce karfin tattalin arzikin attajiran 10 ya karu daga dala biliyan 700 zuwa dala tirimiyan 1 da rabi cikin shekaru 2 kwatankwacin karin dala biliyan 1 da miliyan 300 kowacce rana.

Rahoton na Oxfam na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirin fara taron babban zauren tattalin arziki na Duniya a wani yanayi da tattalin arzikin kasashe da dama ke kokarin durkushewa saboda annobar ta corona.

Dai dai lokacin da hankalin Duniya ya karkata kan yadda za a yaki talaucin da ya yiwa kasashe katutu, rahoton na Oxfam ya ce arzikin attajiran 10 ya hauhawa irin bunkasar da ba a taba gani ya yi ba cikin shekaru 14 da suka gabata tun bayan mashassharar tattalin arzikin da Duniya ta gani a shekarun 1929.

Oxfam ta koka da yadda matsalar rashin daidaitowa da sake talaucewar talakawa ke sabbaba asarar rayukan mutane akalla dubu 21 a kowacce rana a sassan Duniya.

Rahoton na Oxfam ya bayyana cewa rashin samar da daidaito da kuma tabarbarewar tattalin arziki ya kai ga karuwar yunwa a sassan Duniya da yawatar tashe-tashen hankula da nuna wariya ko kuma cin zarafin wani jinsi baya ga gurbacewar muhalli da kuma lalacewar bangaren lafiya.

Alkaluman da rahoton na Oxfam ya tattara ya gano yadda annobar coronavirus ta jefa mutane fiye da miliyan 160 a tsananin talauci.

342/