Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

18 Janairu 2022

13:46:45
1220223

MDD A Mali Ta Dakatar Da Tashin Jiragen Samanta Saboda Takunkuman Tattalin Arzikin

Majalisar dinkin duniya ta dakatar da tashin jiragen samanta a kasar Mali saboda takunkuman tattalin arziki wadanda kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta dorawa gwamnatin sojojin kasar wacce ta dage wa’adin gudanar da zabe a kasar zuwa wasu shekar 4 masu zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - MDD tana da rundunar sojoji kimani 13,000 wacce ake kira MINUSMA a kasar ta Mali, wacce take kokarin murkushe ‘yan ta’adda daga arewacin kasar tun shekara 2013.

Wani mai magana da rundunar ta MINUSMA ya bayyana cewa a halin yanzu suna cikin tattaunawa da gwamnatin kasar ta Mali don sanin sabbin hanyoyin da rundunar zata bi dangane da tafiye tafiyenta. Ya zuwa yanzu dai MINUSMA ta rasa sojoji 230 tun lokacinda ta fara aiki a shekara ta 2013 a arewacin kasar ta Mali.

342/