Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

31 Disamba 2021

13:11:11
1214015

​Alkaluma : Adadin Fararen Hula Da ‘Yan Sandan Amurka Ke Hallakawa Na Dada Muni

Wata kungiyar sanya ido mai zaman kanta dake Amurka, mai lakabin “Mapping Police Violence”, ta ce ’yan sandan Amurka sun hallaka mutane 1,646, bayan hallaka matashin nan bakar fata George Floyd a watan Mayun bara, adadin da ya kai kimanin mutum 3 a duk rana.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wadannan alkaluma dai ba za su yi dadi ga kunnuwan dubban masu zanga zanga, da ’yan rajin kare hakkin al’ummar Amurka ba, musamman ganin yadda suka shafe watanni suna neman a gudanar da sauyi, game da yadda ’yan sanda ke gudanar da ayyukansu bayan kisan Mr. Floyd.

A daya bangaren kuma, masana da dama na ganin alkaluman da kungiyar ta fitar, ba lallai ne su kunshi dukkanin Amurkawa da ’yan sanda ke kashewa a kasar ba.

Kaza lika masu fashin baki na ganin adadin wadanda ke rasa rayukansu a kasar, sakamakon amfani da karfi fiye da kima da ’yan sanda ke yi, ya ma dara adadin da kafofin watsa labarai ke bayyanawa.

342/