Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A watan mayu ne sojojin Isra’ila suka yi ruwan bama- bamai a yankin Gaza na tsawon kwanaki 11 cur, da ya kai ga kashe mutane 260, ciki hard a yara kanana 66, wanda bayan yakin ne mambobi 47 na hukumar kare hakkin bil adama suka amince da fara gudanar da bincike kan laifukan yaki da sojojin Isra’ila suka tafka kan falasdinawa dake zaune a yankunan marasa galihu.
Bayan kada kuri’ar amincewar da jakadan falasdinu na dindindin a majalisar dinkin duniya Riyad Mansur ya yaba da mataki da mambobin majalisar suka dauka na yin watsi da kudurin da Isra’ila game da binciken, kuma ya gode musu game da amincewa da suka yi da kasafin kudin kan batun falasdinu , ciki har da batun kara yawan kudaden da ake bawa hukumar kula da yan gudun hijira falasdinawa ta majalisar Dinkin duniya Unrwa.
342/