Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

20 Disamba 2021

16:26:04
1210514

​Amurka Ta Nada Musulmi A Matsayin Wakilinta Kan Kare ‘Yancin Addinai

Majalisar dattawan Amurka ta amince da ayyana musulmi da Joe Biden ya yi a matsayin wakilin Amurka na farko kan harkokin ‘yancin addini.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Tashar TRT ta bayar da rahoton cewa, a wani mataki wanda shi ne irinsa na farko a kasar Amurka, Majalisar Dattawan kasar ta ayyana Rashad Hussein, Ba'amurke musulmi a matsayin wakilin Amurka kan 'yancin addini.

Rashad Hussein, wanda shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da sunansa a watan Yuli, ya samu amincewar majalisar dattawan Amurka da kuri'u 85 da suka amince da shi, yayin da 5 suka ki amincewa. Hussein shi ne musulmin Amurka na farko da aka zaba a kan wannan mukami.

Rashad Hussein ya taba rike mukamin jakada na musamman a kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da wakili na musamman kan yaki da ta'addanci, da mataimakin mai baiwa fadar White House shawara a gwamnatin tsohon shugaban Amurka Barack Obama.

Kungiyar (CAIR) babbar kungiyar kare hakkin musulmi a Amurka, ta yi maraba da nadin, da cewa: “Wannan rana ce mai cike da tarihi ga al’ummar Musulmin Amurka da kuma al’ummarmu,” a cewar Edward Ahmed Mitchell, mataimakin darektan zartarwa na majalisar a wata sanarwa.

Mitchell ya kara da cewa: "Muna da tabbaci kan cewa Rashad Hussein zai kare 'yancin addini na dukkanin al'ummomin da ke fuskantar barazanar kyama a duniya, ciki har da Musulman Uighur na China."

342/