Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

15 Disamba 2021

14:12:26
1208873

​Amurka Tana Juyayin Mutuwar Mutane 800,000 Sanadiyyar Cutar Covid 19

Kakakin majalisar wakilai ta kasar Amurka Nancy Pelosi ta jagoranci majalisar dokokin kasar a jiya Talata, don bayyana alhani da juyayi na mutuwar mutane kimani 800,000 sanadiyyar cutar Covid 19 a kasar tun bayan bullarta a kasar a shekara ta 2021.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Jaridar the Nation ta kasar Kenya ta bayyana cewa a halin yanzu kasar Amurka tana fama da yaduwar cutar da Covid 19 a kasar karo na 5 kenan. Labarin ya kara da cewa kasar Amurka ce ta fi shan wahala musamman mace-mace sanadiyyar cutar ta Covid 19 a duniyam inda adadin wanda suka rasa rayukansu ya zuwa yanzu ya dara 800,000 a bisa rahoton Jami’ar Hopkins wacce take kula da al-amarin cutar a kasar.

Ance yawan wadanda suka mutu a kasar ya zuwa yanzu ya dare yawan mutane a wu jihohin kasar, wadanda yawan mutanen da suke rayuwa a jihohin basu kai 800,000 ba. Misali jihar Dakota ta Arewa da kuma Alaska.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu sun mutu ne a cikin wannan shekara ta 2021, inda adadinsu ya kai mutane 450,000. Wato fiye da rabin wadanda suka mutu gaba daya. Banda haka mafi yawan wadanda suka mutu ko suke mutuwa daga cikin wadanda suka ki amincewa da ayi masu alluran riga kafin cutar ne.

342/