Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

14 Disamba 2021

18:29:30
1208631

​Amurka: Rundunar Sojojin Sama Ta Sallami Jami’anta 27 Saboda Kin A Yi Masu Alluran Riga Kafin Cutar Covid 19

Rundunar sojojin sama ta kasar Amurka ta bada sanarwan korar jami’anta guda 27 saboda kin a yi masu alluran riga kafin cutar Covid19.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - ya bayyana cewa sakataren tsaron kasar ta Amurka Lloyd Austin ya maida yin alluran riga kafin cutar Covid 19 dole a kan dukkan jami’an sojojin kasar a cikin watan Augustan da ya gabata.

Har'ila yau labarin ya nakalto kakakin rundunar sojojin sama na kasar ta Amurka, Ann Stefanek tana cewa ya zuwa yanzu rundunar sojojin sama na kasar ta rasa jami’anta 79 saboda kamuwa da cutar ta Covid 19.

Wannan dai shi ne karon farko wanda gwamnatin Amurka ta kori sojojinta daga aiki saboda kin a yi masu alluran riga kafin cutar ta Covid 19.

342/