Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

13 Disamba 2021

14:00:23
1208132

Mahaukaciyar Guguwa Ta Kashe Mutum Sama Da 100 A Amurka

A Amurka mutane sama ne ake kyautata zaton sun mutu bayan da wata mahaukaciyar guguwa ta ratsa wasu jahohin kasar da tsakar dare, kamar yadda jami’ai suka bayyana.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Wasu hotuna daga garin Mayfield sun nuna yadda wasu gine-gine suka fada kan titinan mota, yayin da iskar ta tumbuke bishiyoyin da fala-falan wutar lantarki.

A Jihohin Arkansas, Missouri, da Tennessee duk an samu rahoton hasarar rayuka dake da nasaba da mahaukaciyar guguwar.

Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da za ta iya domin taimaka wa jihohin kasar shida da bala'in mahaukaciyar guguwa ya abkawa.

Kafin hakan hukumar hasashen yanayi ta kasar ta sanar da cewa, akalla mutane kusan miliyan 25 suke cikin barazanar fuskantar mummunar iskar da zata ratsa shiyyar.

342/