Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

12 Disamba 2021

10:55:35
1207794

​Amurka: FBI Na Neman Mutumin Da Ke Cinna Wuta A Masallacin New Mexico

Hukumar FBI ta Amurka na neman mutumin da ya cinna wa wani masallaci wuta da kuma cibiyar Musulunci ta New Mexico a lokuta daban-daban.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - A cewar jaridar Albuquerque, Sashen ofishin bincike na tarayya a ranar Laraba ya fitar da hotuna hudu na wata mata da ake zargi da cinna wuta a lokuta da dama a cibiyar Musulunci ta New Mexico. Na'urorin tsaro ne suka dauki wadannan hotuna a ciki da wajen ginin.

Raul Bojanda, jami'i na musamman da ke kula da sashen ya ce "Muna mutunta masu gudanar da harkokinsu na addini a cikin wannan cibiyar Musulunci ta New Mexico, kuma ba za mu iya jure wa irin wannan dabi'ar ta'addanci ba." Muna fata duk wanda ya san wanda yake aikata haka zai tuntube mu da wuri-wuri.

A farkon ranar 29 ga watan Nuwamba, matar ta cire kayan da ake iya konawa a cikin kwandon shara a wajen masallacin, ta banka masa wuta a kusa da kofar shiga. Ta kuma dauko wuta tana kokarin cinnawa a cikin farfajiyar ginin, kuma Masu shaguna da ke kan titin sun ga hayaki na tashi inda suka taimaka wajen kashe wutar da ruwa kafin ma’aikatan kashe su iso.

A ranar 7 ga watan Nuwamba ma, wannan mata ta shiga cikin ginin cibiyar musluncin a lokaciin da babu kowa da misalin karfe 9:00 na safe, inda ta yi kokarin cinna wuta a kan kafet din masallacin cibiyar.

A cewar mai magana da yawun cibiyar Musulunci, daya daga cikin daliban da ke cikin masallacin ya ga matar sai ta buga kararrawa, lamarin da ya sa ta gudu tana ta yin kalaman batunci a kan addinin musulunci da musulmi.

342/