Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

12 Disamba 2021

10:54:31
1207792

​Babban Zauren MDD Ta Amince Da Wasu Kudurori 5 Na Goyon Bayan Falastinu

Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da kudurori biyar na goyon bayan Falasdinu da kuma adawa da gwamnatin sahyoniyawan da kuri'u mafi rinjaye.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Shafin jaridar Al-raya ya bayar da rahoton cewa, Kudurin farko ya shafi kare 'yan gudun hijirar Falasdinu, wanda kasashe 164 suka amince da shi.

Kudiri na biyu dai yana da alaka ne da ayyukan hukumar ba da agajin ‘yan gudun hijira ta Falasdinu (UNRWA) da kuri’u 162 suka amince da shi, 5 na adawa da 6 kuma suka ki kada kuri'a, kuma kuduri na uku shi ne kan ‘yan gudun hijirar Falasdinu da kudaden shigar da suke samu a nan gaba da kuri’u 159 zuwa, kasashe 5 na adawa da kurin, takwas sun ki kada kuri'a a kansa.

Kuri'a 146 ne suka amince da kuduri na hudu kan rashin hakascin gina matsugunan yahudawan sahyoniya a yankunan Falasdinawa da suka hada da Gabashin Kudus da kuma yankin Golan na Siriya da aka mamaye.

Kudiri na biyar kuma na karshe da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi yana magana ne kan ayyukan kwamitin bincike na musamman kan ayyukan kare hakkin bil'adama kan ayyukan cin zalun na Isra'ila a kan al'ummar Palastinu da kuma Larabawa mazauna yankunan da ta mamaye, wanda kasashe 80 suka amince da shi; Yayin da kasashe 73 suka ki amincewa da shi, wasu kasashe 18 kuma suka ki kada kuri'a a kansa.

342/