Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

10 Disamba 2021

18:52:30
1207208

MDD: An Samar Da Kudurin Mai Yin Allawadai Da Ayyukan Isra’ila A Kasar Siriya

A safiyar Jumma’a ce babban zauren mdd ta amince da wani kuduri mai yin allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) dangane da mamayan da take yiwa yankin tuddan Golan na kasar Siriya da babban rinjaye.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- ya kara da cewa kasashe 149 ne suka amince da kudurin wanda ya bukace HKI da dakatar da duk abinda take a yankunan tuddan Golan na kasar Siriya. Sannan kudurin ta bayyana cewa duk abinda take yi a yankin ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Wakilan kasashen Amurka da kuma haramtacciyar kasar sun ki amincea da kudurin sannan wasu kasashe 23 sun ki kada kuri’unsu.

342/