Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

4 Disamba 2021

14:52:01
1205145

​An Yi Amfani Da Manhajar Kamfanin NSO Na Isra’ila Wajen Yin Kutse A Wayoyin Jami’an Amurka

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, an yi amfani da manhajar kamfanin NSO na isra’ila wajen yin kutse a cikin wayoyin hannu na wasu jami’an gwamnatin Amurka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Rahoton na kamfanin dillancin labaran reuters ya ce, an yi amfani da manhajar ne wajen kutsawa a cikin wayoyin jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka, tare da yin leken asiri a cikin bayanan da wayoyin nasu suke dauke da su.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, bayanan da aka yi kutse a cikinsu sun shafi kasar Uganda ne, duk kuwa da cewa rahoton ya ce ba a iya gane takamaimai wanda ya yi amfani da manhajar wajen yin wannan aikin leken asiri ba.

Sai dai a nasa bangaren kamfanin na NSO na Isra’ila ya sanar da cewa, ba shi da masaniya kan a bin da ya faru, amma zai gudanar da kwakkwaran bincike kan lamarin, sannan kuma idan aka gano jami’in leken asirin da ya yi amfani da manhajar ta NSO, to za a dakatar da yin aiki tare da shi, sannan kuma za a dauki matakai na shari’a a kansa.

Sai dai a nata bangaren ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka taki ta ce uffan a kan wannan batu, duk kuwa da cewa wannan ba shi ne karon farko da ake bankado ayyukan leken asirin da Isra’ila ke yi kan jami’an gwamnatin Amurka ba.

342/