Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

29 Nuwamba 2021

19:33:20
1203498

MDD:Yanayin Da Yankin Falasdinu Ke Ciki Babban Kalubale Ne Ga Duniya

Babban sakatare Janar din majalisar dinkin duniya Antonio Gutterres ya fadi a lokacin bukin ranar nuna goyon baya ga Al’ummar Falasdinu cewa ‘yanayin da ake ciki a yankin falasdinu da HKI ta mamaye ya kasance babban kalubale ga zama lafiya da tsaro a duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ya kara da cewa a ranar nuna goyon bayan Al’ummar falasdinu yana da kyau mu kara jaddada matsayinmu ga alummar falasdinu a fafutukar da suka yi ta kwatar yanci da gina kyakkyawar makoma a nan gaba, mai cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakaninsu da Isra’ila

Tun a shekara ta 1977 ne Majalisar dinkin duniya ta ayyana ranar 29 ga watan Nuwamba a matsayin ranar nuna goyon baya ga Alummar Falasdinu kamar yadda kuduri mai laman 32/40 ya tabbatar

A wannan ranar ce a shekara ta 1947 babban zauren majalisar ya amince da kuduri mai lamba 181 game da halin da yankin Falasdinu inda suka rasa gidajensu bayan da yahudawa suka mamaye yankin tare da kafa HKI .

342/