Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

24 Nuwamba 2021

19:42:36
1201854

​Majalisar Dinkin Duniya Ta Zargi Amurka kan Take Hakkin Al’ummomi Marasa Rinjaye A Kasar

A cikin wani rahoto da Majalisar ta fitar ya nuna cewa kasar Amurka tana tinkaho da cewa kasa ce ta yanci musamman na dimokuradiya da walwala.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : To sai dai lamarin ya sha bamban game da yadda kwararre kan kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya ga lamarin, ziyarar da kwararren ya kai a baya bayan nan a kasar Amurka ya fahimci abubuwa da dama.

Ya ce Alummomi marasa rinjaye a kasar ana mayar da su saniyar ware musamman idan aka zo batun da ya shafi hakkin kada kuri’a da kuma basu damar amfani da ababen more rayuwa na gama gari.

342/