Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

24 Nuwamba 2021

19:40:04
1201850

Har Yanzu Akwai ‘Yan Siyasar Da Ake Tsare Da A Sudan

A Sudan, har yanzu tsugunne ba ta kare ba, kwanaki uku bayan cimma yarjejeniya tsakanin shugaban mulkin rikon kwarar soji na kasar Janar Al-Burhane da kuma shugaban gwamnati Abdallah Hamduk da aka mayar kan mukaminsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kawo yanzu 12 daga cikin ministoci 17 na hadakar samar da ‘yanci da sauyi a kasar sun mika takardar murabus dinsu hannu da hannu ga shugaban gwamnatin Abdallah Hamdok.

Haka zalika kungoyi da daman a farar hula sun yi watsi da yarjejeniyar da aka cimma da sojojin masu juyin mulki.

Duk da cewa bai yaba da yarjejeniyar dari bisa dari ba, Abdollah Hamduk ya kare matakin da ya dauka da cewa zai bada damar lalubo bakin zaren warware rikicin kasar.

Yarjejeniya ce mai kyau wacce za ta iya aiki da ita kamar yadda ya bayyana a wata hira da tashar talabijin ta CNN, kwana uku bayan komawa kan mukaminsa .

Ya ce zai yi aiki kan shirye shiryen zaben kasar na 2023, kamar yadda aka tsara a yarjejeniyar zaman lafiya.

342/