Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A sabon rahoton da ta fitar hukumar ta ce, annobar korona, canjin yanayi da rikice rikice sun yi tasiri sosai kan harkar samar da abinci musamman a nahiyar Afrika.
A yankin kudancin Afrika, sama da mutane miliyan 80 ne zasu iya rasa samun abinci mai kyau idan aka fuskanci wani sabon tashin hankali a cewar FAO.
Dole ne kasashen da matsalar ta shafa su gabatar da wani da ya shafi abincin da suke samarwa a gida da wanda suke shigo da shi.
342/