Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

22 Nuwamba 2021

13:19:34
1201143

Amurka : Mutum 5 Sun Mutu, Yayin Da Wani Mutum Ya Abka Musu Da Mota

Rahotanni daga Amurka na cewa mutane akalla biyar ne suka mutu, kana wasu kimanin arba’in suka raunana yayin da wani mai mota dake gudun tsiya ya abka masu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Lamarin ya faru ne a wani wurin faretin shagulgulan bikin Kirsimeti a jihar Wiscusin.

Mahukunta sun ce an wuce da mutun 23 asibiti inda 12 daga ciki yara ne.

Kawo yanzu dai ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma ‘yan sanda sun ce sun gano wata mota da ake zargin ita ce aka yi amfani da ita wajan kai wannan hari.

Haka kuma ‘Yan sanda sun ce sun kama wani mutum da ake zargin yana da hannu a cikin alamarin sai dai ba su yi karin haske ba.

342/