Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Har ilya yau da yake bayani a Helkwatar hukumar habaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWA) Blinken ya bukacin kasashen yammacin Afrika da su yi watsi da mulkin kama karya, kuma su tabbatar an ingantaccen tsarin Dimokiradiya a kasashensu.
Blinken da yake ziyararsa ta farko a yankin kudu da Hamadar sahra a matsayinsa na sakataren wajen kasar Amurka ya fadi cewa kungiyoyi irin su ECOWAS, AU, SADAC da IGAD ya kamata su taka muhimmiyar rawa da ta dace, kuma su kasance suna da karfin fada a ji a muhawarorin da ake yi a duniya.
342/