Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

20 Nuwamba 2021

14:52:08
1200475

​Najeriya: Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Kai Ziyarar Aiki A Abuja

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa da takwaransa na Nigeria Geoffrey Onyema, inda ya bayyana damuwar kasarsa akan batun kare hakkin dan’adam a cikin kasar ta Nigeria.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Bugu da kari sakataren harkokin wajen na Amurka ya nuna goyon kasarsa akan yadda ya kamata Nigeria ta taka gagarumar rawa a cikin nahiyar Afirka,kamar kuma yadda ya yaba da yadda alaka a tsakanin nahiyar Afirka da kasarsa take kara bunkasa.

A ranar Alhamis ne dai sakataren harkokin wajen na Amurka Anthony Blinken ya ziyarci Nigeria bayan kasar Kenya wadda ita ce ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka tun bayan da jam’iyyarsu ta Democrat ta kafa gwamnati.

Jim kadan bayan isarsa Nigeria din ne dai sakataren harkokin wajen na Amurka ya gana da shugaba Muhammadu Buhari, inda su ka tattauna batun halayyar keta ta ‘ yan sandan kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa bakon nashi cewa; Gwamnatin tarayya tana bin ka’ida wajen gudanar da bincike kuma tana gudanar da ayyukanta ne a fili ba a boye ba.

342/