Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

18 Nuwamba 2021

11:32:51
1199781

​Wata Kotu A Murka Zata Wanka Mutane Biyu Wadanda Ake Tuhuma Da Kashe Malcolm X

A yau Alhamis ce ake saran wata kotu a unguwar Manhattan na birnin New York a kasar Amurka za ta wanke mutane biyu wadanda ake tuhuma da kashe sanennen dan rajin kare hakkin bakaken fatar kasar Malcolm X kimani shekaru 60 da kashe shi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Aljazeera daga birnin Doha na kasar Qatar ta nakalto wani jami’in tsaro na kasar yana fadar haka a jiya Laraba. Labarin ya kara da cewa mutanen biyu wadanda suka hada da Muhammad Abdul-Aziz da kuma Khalil Islam wanda kafin haka ake kiransu Norman 3X da kuma Thomas 15X sun ce ba su da hannu wajen kashe Malik Al-shabbas ko Malkcon X a shekara 1964.

Masu bincike a Manhatan sun biyya cewa bayan sun sake duba takardun karar da aka shigar kan kissan Malcom X sun gano cewa an boyewa alkali wanda ya yankewa wadanda ake tuhumar hukuncin daurin rai-da rai a shekara 1966. Akwai yiyuwan ba su suka kashe Malik Al-shabas ba, don haka a yau ana iya sallamarsu daga gidan kaso bayan sun share shekari kimani shekaru 60 a gidan kaso.

342/