Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

18 Nuwamba 2021

11:27:03
1199774

​Guterres Ya Bayar Da Shawarar Mika Wani Bangaren Birnin Quds Ga ‘Yan Mamaya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a amince da bangaren birnin Quds a matsayin mallakin yahudawan sahyoniya, yayin da kuma rabin birnin zai kasance mallakin Falastinawa a hukumance, ta hanyar yin alkawurra tsakanin bangarorin biyu, domin warware matsalar Falasdinu da Isra’ila.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a sasanta bangarorin biyu da basa ga maciji da juna ta hanya daya tilo, wato cimma muradun al'ummar Falasdinu na kafa kasarsu ami cin gashin kanta, tare da baiwa Isra’ila wani bangare na birnin Quds bisa yarjejeniya tsakaninsu.

A yayin wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu da aka fara yau a hedkwatar MDD dake birnin New York kan batun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, Guterres ya yi kira ga shugabannin Isra'ila da na Falasdinu da su nuna azama ta siyasa wajen farfado da tattaunawa a tsakaninsu.

Ya kara da cewa: taron na bana ya zo daidai lokacin cika shekaru 30 na taron zaman lafiya na Madrid, wanda lokaci ne mai cike da tarihi inda aka yi shawarwari tsakanin Isra'ila da Falasdinu da kuma kafa harsashin samar da zaman lafiya da ya kamata a yi kokarin cimmawa.

"Majalisar Dinkin Duniya ta kuduri aniyar yin aiki tare da Isra'ila da Falasdinawa da abokan huldarsu na kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ciki har da yankin Gabas ta Tsakiya, don cimma wannan buri."

An kafa kwamitin tuntubar juna kan wannan batu a shekara ta 2002, wanda ya hada da Rasha, Amurka, Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya.

Tun a watan Afrilun shekara ta 2014 ne dai aka dakatar da tattaunawa tsakanin Falastinawa da gwamnatin Sahayoniya, saboda kin amincewa da Tel Aviv ta yi na sakin tsofaffin fursunoni, da dakatar da gini matsugunnan yahudaw, da kuma amincewa da iyakokin da aka yi kafin yakin watan Yunin 1967 a matsayin tushen samar da kasashe biyu.

342/