Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

16 Nuwamba 2021

19:00:13
1199171

​MDD: Kashi 75 % Na Mutanen Yemen Na Fama Da Karancin Abinci

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadi cewa kimanin kaso 75% na alummar kasar Yamen ne ke fama da matsalar karancin Abinci. Mmusamman yara kanana, saboda ci gaba da kai hare-haren da Saudiya da kawayanta su ke kaiwa kan kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Majalisar ta yi kira ga masu fada a ji na duniya da su sanya baki a kawo karshen zubar da jinni da ake yi a kasar. A cikin wani bayanin da ta wallafa a shafinta na Twiter WHO ta yi gargadin cewa a duk daya daga cikin yara 3 na kasar Yamen ya na fuskantar matsalar karancin abinci mai gina jiki, wanda ya ke bukatar taimakon gaggawa .

Duk da alkawarin da kasar Amurka ta yi a watan fabareru na kawo karshen dukkan goyon bayan da take bawa Saudiya a yakin da take yi a Yamen, wanda ya hada da dakatar da sayar mata da makamai, basu tabbata ba. Banda haka sai ga shi a bayan bayan nan shugaban Amurka Joe Baiden ya amince a sayar wa Saudiya muggam makamai wadanda kudinsu ya kai dalar Amurka miliyon $650.

342/