Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : M. Guteress, ya ce, har yanzu akwai sauren jan aiki kafin a tsira daga faruwar iftila'in dake faruwa sanadin sauyin yanayi.
Babban sakataren na MDD, ya yi wannan furicin ne bayan kammala taron koli na sauyin yanayi.
A karshen taron dai na Glasgow, kasashen duniya sun amince su rage a mai makon kawar da amfani da kwal bayanda wasu suka nuna rashin jin dadinsu.
Shugaban taron na COP26, Alok Sharma ya ce '' ya yi matukar nadama'' a kan yadda abubuwa suka faru. Sai dai ya ce yana da matukar muhimmanci a kare yarjejeniyar baki daya.
Taron kolin sauyin yanayi na MDD ya kammala a ranar Asabar bayan tsawaita wa’adin taron da kwana guda, inda mahalarta taron suka amince da sabuwar yarjejeniyar kasa da kasa game da yadda za a tinkari batun magance matsalolin sauyin yanayi.
342/