Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

14 Nuwamba 2021

11:47:05
1198400

​An cimma sabuwar yarjejeniya kan sauyin Yanayi ta Duniya a taron Glasgow

Rahotanni dake fitowa daga Glasgow na nuna cewa an kawo karshen taron kilo na kasashen Duniya kan sauyin yanayi na Cop 26 kuma an cimma yarjejeniyoyi masu muhimmanci da za su taimaka wajen shawo kan matsalar dimamar yanayi matukar aka yi aiki da su.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wannan dai it ace yarjejeniyar ta farko a irinta da aka cimma da fayayce hanyoyin da za’a bi wajen ganin an rage tasirin dimamar yanayi musamman yawan yin amfani da kwal da shi ne yafi gurbata yanayi a duniya. Kuma za’a rage yawan dumamar yanayin da maki 1.5 a maaunin salshes

A na sa bangaren sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterres yace lokacin yayi da ya kamata a dauki mataken gaggawa na dakile matsalar dumamar yanayin ta hanyar yawan yin amfani da hayaki mai gurbata muhalli idan ba haka bah aka ba za ta cimma ruwa ba,

Daga karshe dukkan kasahen sun alkawarin sake ganawa a shekara mai zuwa domin sake bita kan alkawurin da ak dauka na rage yawan hayakin mai gurbata muhalli yadda za’a cimma burin da ake da shin a rage matsalar zuwa kashi 1.5

342/