Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

14 Nuwamba 2021

11:42:53
1198399

​An Zargi Amurka Da Kokarin Haifar Da Fitina A Iraki Ta Hanyar Kashe Manyan ‘Yan Siyasar Kasar

A wata hira da gidan talbijin na Al’Malouma ya yi da wani mamba a kwance kungiyar Fata a majalisar kasar iran Mohammad Albaldawi ya yi gargadi game da makircin da Amurka ke kullawa na yunkurin haifar da fitina a Iraki ta hanyar kashe manyan yan siyasar kasar tare da dora alahaki kan kungiyoyin gwagwarmaya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ya na mai cewa rahoton da aka fitar game da harin da aka kai da jirgi mara matuku kan gidan fira ministan Iraki da aka tabatar ya daga ofishin jakadancin Amurka ne dake bagadaza na tabbatar da hakan

Har ila yau yau nuna takaicinsa game da jan kafa da gwamntin kasar take yi wajen gudanar da binciken gano hakikanin gaskiya kan yunkurin kisan gillan da aka yi wa fira ministan kasar Mustapha Al’kazimi.

Daga kareshi yace Amurka ta san dukkan jami’an tsaro day an siyasar kasar don haka dukkan su suna cikin hadari, domin a kowanne lokacin Amurka tana iya kai musu hari kuma ta dora alhaki kan kungiyoyin gwagwarmayar kasar domin kunna wutar rikici a kasar