Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

11 Nuwamba 2021

15:49:51
1197665

Sin Da Amurka Sun Amince Inganta Matakan Yaki Da Sauyin Yanayi

Kasashen Amurka da Sin, sun fitar da sanarwar hadin gwiwar Glasgow, kan habaka matakan yaki da sauyin yanayi, a ci gaba da zama na 26 na taron bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD wato (COP26) a Glasgow.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Bangarorin biyu sun yi alkawarin ci gaba da yin aiki tare da dukkan sassa, don karfafa aiwatar da yarjejeniyar Paris.

Sun kuma amince su kafa kungiyar aiki kan inganta matakan yaki da sauyin yanayi a shekarun 2020, don inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da kuma hanyoyin da za a bi.

MDD, ta bakin babban sakatarenta, Antonio Guterres, ta yi maraba da kasashen biyu, game da inganta matakan yaki da sauyin yanayi a taron Glasgow.

M. Guterres ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa, "Ina maraba da yarjejeniyar da Sin da Amurka suka fitar, don yin aiki tare ta nufin kara cimma burin da aka sanya a gaba bisa maudu’in #ClimateAction, a cikin wadannan gwamman shekaru,".

Yana mai cewa, idan har ana bukatar magance matsalar sauyin yanayi, akwai bukatar kasashen duniya su hada kai, kuma wannan mataki ne mai muhimmanci a kuma lokacin da ya dace.

342/